Dangote ya kai ƙarar tsohon shugaban NMDPRA zuwa EFCC

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kai ƙarar tsohon shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur ta Najeriya, NMDPR, Farouk Ahmed, gaban EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito wata sanarwa daga kamfanin Dangoten, cewa shugaban kamfanin ya shigar da ƙarar Farouk a shalkwatar hukumar ta EFCC.

A baya Dangote ya shigar da ƙarar Forouk gaban hukumar ICPC mai yaƙi da almundahana a Najeriya, domin bincikarsa kan zargin kashe dala miliyan biyar wajen karatun sakandiren ƴaƴansa a ƙasar Switzerland.

Sai dai a kwanakin da suka gabata ne Dangote ya janye ƙorafin nasa daga hukumar ICPC, kodayake hukumar ta ce za ta ci gaba da binciken nata.

Sanarwar Dangoten ta ce ta janye ƙorafin daga ICPC ne domin samun damar shigar da sabon ƙorafi gaban hukumar EFCC.

A ƙorafin nasa Dangote ya buƙaci EFCC ta binciki Farouk bisa zargin tafka almundana da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba, tare da gurfanar da shi a gaban kotu idan aka same shi da laifi.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere