Majalisar Dokokin Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara

Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta fara shirye-shiryen tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, lamarin da ya haddasa ruɗani a siyasar jihar.

A zaman majalisar na ranar Alhamis, da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, ya jagoranta, Shugaban Masu Rinjaye, Major Jack, ya karanta takardar zargin da ake yi wa gwamnan bisa aikata manyan laifuka.

Ya danganta yunƙurin nasu da Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Daga cikin zarge-zargen da ake yi wa Gwamna Fubara, akwai rushe ginin Majalisar Dokokin, kashe kuɗaɗen gwamnati ba tare da amincewa da kasafin kuɗi ba.

Sauraun sun haɗa da hana kuɗaɗen da aka ware wa Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dokokin jihar, da kuma ƙin bin hukuncin Kotun Ƙoli kan ’yancin kuɗaɗen Majalisar.

’Yan majalisa 26 ne suka sanya hannu a kan takardar neman tsige gwaman.

Kakakin majalisar ya ce za su aike wa gwamnan da takardar cikin kwanaki bakwai.

Bayan haka, Mataimakiyar Shugaban Masu Rinjaye, Linda Stewart, ta gabatar da wata takardar zargi kan Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Ngozi Odu.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.