Rundunar ƴan sandan Kano ta kama mutane uku da ake zargi da fashi da makami

Rundunar ƴan sandan Kano ta kama mutane uku da ake zargi da fashi da makami

‎Sanarwar hakan na kunshe cikin sanarwar da kakakin Rundunar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a daren yau.

‎Sanarwar ta kara da cewa jami’an ƴan sanda sun cafke Isyaku Maude mai shekaru 37, wanda aka fi sani da Dan Sokoto, bayan samun sahihan bayanan sirri, inda ya amsa aikata jerin fashi da makami a birnin Kano.

‎Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga cafke wasu mutane biyu, Sahabi Danladi mai shekaru 20 da Najib Ibrahim mai shekaru 32.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.