Babban Labari

An kama ɓarauniyar jariri a asibiti a Zamfara.

An kama wata matashiya ’yar shekara 27, kan zargin satar jariri mai kwana 10 da haihuwa a Babban Asibitin Ƙaura Namoda da ke Jihar Zamfara. Dubun wadda ake zargin ya cika ne kwanan da sace jaririn, inda ’yan sanda suka fara gudanar da bincike bayan samun rahoton. Bayanan samun ƙorafin ne Babban Ofishin ’Yan Sanda […]

Read more

Yusuf Buhari ya lashe zaɓen takarar majalisar tarayya a APC

Yusuf Buhari, ɗan tsohon shugaban Najeriya marigayi Muhammadu Buhari, ya samu nasara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC na mazabar Sandamu/Daura/Mai’adua. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin zaɓe na mazabar, Lawan Garba, ya ce Yusuf Buhari ya samu ƙuri’u 17,342, inda ya doke abokin takararsa, Auwalu Musa Daura, wanda ya samu ƙuri’u […]

Read more

Man City ta lashe kofin FA bayan doke Chelsea 1-0

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin FA na shekarar 2026 bayan doke Chelsea 1-0. Antoine Semenyo ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Man City nasara bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Wannan ne kofi na biyu da ƙungiyar ta lashe a kakar wasa ta bana bayan lashe kofin Carabao […]

Read more

Adadin ɗabilan da aka sace daga Borno sun kai 50

Bayanan da ke fitowa daga Najeriya na cewa fiye da ɗalibai 50 ne aka bayar da rahoton garkuwa da su a wasu hare-hare da aka kai wa makarantu a yankin arewa maso gabashin ƙasar aranar Juma’a Rahotonni na cewa mafi yawan yaran ƴan tsakanin shekara biyu zuwa biyar ne, waɗanda aka sace daga makarantun nazare. […]

Read more

Jami’an kwastam biyu sun mutu a fafatawa da Lakurawa

Jami’an hukumar kwastam biyu sun rasa ransu a fafatawar da suka yi da mayaƙan da ake zargi Lakurawa ne a jihar Kebbi. Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an masu muƙamin ASC da DSC, sun rasa ransu ne yayin samamen […]

Read more

Tsohon Shugaban ’Yan Sanda ya janye daga takarar Gwamnan Yobe

Tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alƙali, ya sanar da janyewarsa daga neman takarar Gwamnan Jihar Yobe. Usman Baba Alƙali wanda ke neman takarar Gwamnan Yobe a ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC, ya sanar da haka ne ta wata takardar sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Ya bayyana cewa ya yanke shawarar janyewa ne […]

Read more