Babban Labari

Gwamnonin Arewa sun yi alhinin rasuwar matar Farfesa Jega

Gwamnonin jihohi 19 na Arewacin Najeriya sun miƙa ta’aziyyarsu ga tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Hadiza. Hajiya Hadiza ta rasu ne a ranar Lahadi, kuma an yi jana’izarta bisa koyarwar addinin Musulunci bayan gudanar da sallar jana’iza a Masallacin Ƙasa da ke Abuja. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin […]

Read more

Kalaman Wike Na Barazanar Harbin Ɗan Jarida Sun Tayar Da Ƙura

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya tsinci kansa a tsaka mai wuya, biyo bayan barazanar harbin ɗan jarida yayin da ake tsaka da gabatar da shiri a gidan talabijin. Wike ya yi wa fitaccen ɗan jaridar gidan talabijin na Channels, Seun Okinbaloye, barazanar harbi, lamarin da ya fusata ƙungiyoyin ’yan jarida da na kare […]

Read more

Ƙaramar ministar ƙwadagon Najeriya ta yi murabus

Ƙaramar Ministar kwadagon Najeriya Nkeiruka Onyejeocha ta yi murabus daga muƙaminta. Ta sanar da murabus ɗin nata ne a shafinta na X, inda ta miƙa godiyarta ga shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya bata dama ta yi aiki da gwamnatinsa. Ta bayyana ajiye muƙamin nata a matsayin matakin rufe wani gagarumin babi na rayuwarta a […]

Read more

Tarko INEC ke son ɗana mana kuma ba za mu kamu ba – ADC

Jama’iyyar adawa ta ADC ta haɗakar ƴan adawar Najeriya ta zargi hukumar zaɓen ƙasae INEC ta naɗa mata tarko ta hanyar hanyar yunƙurin dakatar da ita daga gudanar tarukanta domin zaɓen shugabanninta. ADC – tsagin David Mark – ta jaddada aniyar ci gaba da tsare-tsarenta na gudanar da zaɓukan shugabanninta na jihohi da babban taron […]

Read more

INEC ta yi watsi da kiraye-kirayen cire shugabanta

Hukumar zaɓen Najeriya ta yi watsi da kiraye-kirayen da wasu ke yi wa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya sauka daga muƙaminsa. Cikin wata sanarwa da INEC ɗin ta fitar ta bayayna kiraye-kirayen da hari kan dokokin da suka kafa hukumar. A ranar Alhamis ne jam’iyyar ADC mai hamayya a ƙasar, ɓangaren David Mark ta […]

Read more

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya raba tallafin ₦8,431,768.80 ga iyalan yan sandan da suka rasu.

Rundunar ‘ƴan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin , CP Ibrahim Adamu Bakori,  ta raba Cek ɗin kuɗi Naira miliyan takwas da dubu ɗari 431 da 768 da kobo 80 (₦8,431,768.80) ga iyalan jami’an rundunar 18 da suka rasu. Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar CSP Abdullahhi Haruna Kiyawa, ya bayyana ta cikin wata […]

Read more