Home » CBN Ya Amince da Hukuncin Kotun Koli

CBN Ya Amince da Hukuncin Kotun Koli

Soludo/Kan Batun Tsofaffin Takardun Kudi

by Anas Dansalma
0 comment

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya amince bai wa bankunan kasuwanci umarnin su fitar da tsoffin takardun kudade kuma su karbi tsoffin muddin kwastomomi suka kawo musu, kamar yadda gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Charles Soludo wanda tsohon gwamna babban banki ya bayyana.

Gwamnan ya ce, yanzu mutane na da damar zuwa bankuna su shigar da takardun kudadensu tsofaffi ba tare da wani ƙayyadadden lokaci ba.

Gwamnan babban bankin ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin wata ganawa da kwamitin bankuna da ya gudana a jiya Lahadi.

Wannan na zuwa ne bayan da shi Soludo ke tabbatar da wannan umarni na Gwamnan babban bankin, inda ya tabbatar da samun wannan labari ne ta wayar tarho da ya yi da gwamnan a daren jiya.

Tsohon gwamnan babban bankin ya kuma buƙaci kuma bukaci al’ummar jihar da su kai rahoton duk wani bankin da yaƙi amsar tsofaffin kudi.

Sai dai majiyarmu ta yi ƙoƙarin jin ta bakin  kokarin da aka yi don jin ta bakin Kakakin babban bankin Isa Abdulmumin domin tabbatar da ikirarin na Soludo, sai dai hakan ya citura.

Har’ila yau wasu majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa tabbas an yi wannan ganawa da gwamnan babban bankin da wasu manyan jagororin bankuna a ranar Lahadi don haka babu mamaki idan Saludo ya ba da wannan tabbaci.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi