Cikin Hotuna: Halin Da Makarantar Taraunin Kudu Ke Ciki A Kano

Yayin da harkar Ilimi a Najeriya ke ci gaba da fuskantar
matsaloli,  wasu makarantun gwamanati a jihar Kano sun
koka kan halin da makarantunsu ke ciki.

Wanna  na zuwa ne yayin da wata makarantar Sakandare
dake  karamar  hukumar  Tarauni , ta bayyana
fargabarta game da makomar karatun yara,  sakamakon
zargin da ake yiwa wasu batagarin matasa na shiga
makarantar suna sace-sace da shaye-shaye sakamakon
lalacewar ginin makarantar.

Haka zalika matsalar rashin Katanga a Karamar ta Taraunin Kudu, na kara barazana ga ilimin yaran yankin, saboda sace-sace da shaye-shaye harma da yin bayan gida a wasu daga cikin ajujuwan makarantar.

Mazauna kusa da makaranatar sun bayyana cewa cikin dare ake sace Kofofi da Tagogin makarantar saboda rashin masu gadi, kuma suna yin bakin kokarinsu wajen dakile faruwar abubuwa mara kyau a makarantar.

Karamar makarantar sakandiren ta taraunin kudun a yankin karamar hukumar Tarauni Kano, na cikin rashin tsafta da rashin ingantaccen yanayin koyo da koyarwa saboda warin bayan gida da kuma rashin kujerun zama ga dalibai, sai matsalar sace-sacen kayan makarantar duk saboda da rashin Katanga da masu gadi.

Alhaji Muhd Nura Abdullahi, shi ne dagacin Tarauni, ya bayyana cewa matsalar makarantar bai sanya sun nannade hannunsu ba, domin sun bi duk inda ya kamata su kai kukansu amma har yanzu babu wani abu da aka yi akan matsalarsu.

Dagacin Tarauni Alhaji Muhd Nura Abdullahi

Ya kara da cewa yanzu haka batagarin matasa na balle kwanon rufin makarantar harma da fasa gini don cire rodin da aka yi amfani wajen yin ginin.

A karshe sun yi kira gagwamnatin ta dauki matakin gaggawa kan matsalar.

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya