Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci jami’an rundunar da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da rikon amana, tare da kauce wa karɓar cin hanci da rashawa.
CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai Area Command Wudil, inda ya gana da dakarun da ke aiki a yankin.
Ya kuma yi kira ga jami’an da su riƙa gaggauta amsa kiran neman agaji sannan su faɗaɗa sintiri , tare da kauce wa duk wani hali da ya saɓa wa ƙa’idojin aikin ƴan sanda.
Ziyarar na zuwa ne bayan irin wadda kwamishinan ya kai, Area Command Bichi da Ɗanbatta, da nufin ƙarfafa ayyukan tsaro da kuma inganta alaƙa tsakanin ƴan sanda da al’umma.
CP Bakori ya ce ziyarar ta yi daidai da umarnin Babban Sufeton ƴan sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, na inganta aikin ƴan sanda mai dogaro da bayanan sirri, kare haƙƙin ɗan Adam da kuma kyautata hidimar tsaro ga jama’a.
Ya kuma yaba da ƙoƙarin jami’an rundunar yankin Wudil wajen yaƙi da laifuffuka, tare da tabbatar musu da cewa rundunar na ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren inganta walwala da jin daɗin jami’ai.
A nasa jawabin, Kwamandan ƴan sandan Wudil, ACP Hussaini Yalwa Mohammed, ya yaba da ziyarar kwamishinan, yana mai tabbatar da cewa za su ƙara himma wajen gudanar da ayyukansu.