Mahukuntan lafiya a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DR Congo) sun sanar da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon ɓullar cutar Ebola nau’in Bundibugyo ya kai 506.
Tun bayan ayyana ɓarkewar cutar a ranar 15 ga Mayun 2026, an tabbatar da kamuwar mutum 1,561, yayin da mutum 628 ke killace ko kwance a asibiti a larduna uku na gabashin ƙasar.
Lardin Ituri ne har yanzu ke kan gaba wajen yawan waɗanda suka kamu da cutar, inda yake da fiye da kashi 90 cikin 100 na dukkanin waɗanda aka tabbatar sun kamu.
Haka kuma jami’an lafiya sun nuna damuwa kan yawaitar zirga-zirgar jama’a a yankunan da ke cikin haɗari, musamman sakamakon rikice-rikice da ayyukan haƙar ma’adinai.
Barkewar cutar ta kuma shafi ma’aikatan lafiya, inda mutum 96 daga cikinsu suka kamu da cutar, yayin da 19 suka mutu. Duk da ƙarancin kayan kariya da matsalolin da ake fuskanta, jami’an lafiya sun ce ana samun ci gaba wajen bibiyar mutanen da suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar, kuma adadin waɗanda suka warke ya kai 254.