Ana hasashen yiwuwar rikici tsakanin Amurka da Iran

Ana ci gaba da nuna damuwa kan yiwuwar sake barkewar rikici tsakanin Amurka da Iran, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana rashin gamsuwarsa da bukatun da Iran ta gabatar a tattaunawar da ke gudana.

Wani babban jami’in soja a Iran ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar sabon rikici ya ɓarke, yana mai cewa halin da ake ciki na iya rikidewa idan ba a samu matsaya ba.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na Iran sun ce Tehran ta gabatar da wani sabon daftari ga Pakistan, wadda ke taka rawa a matsayin mai shiga tsakani, sai dai ba a bayyana cikakken bayani kan abin da daftarin ya kunsa ba.

Post masu alaƙa

Sai ’yan Najeriya sun sayi litar man fetur N5,000 idan Tinubu ya zarce

Kotu ta dage hukunci kan shari’ar datse yatsa bisa alkawarin naira miliyan 80.

Farashin mai ya ɗaga a duniya bayan soke tattaunawar Iran da ƙasashen Gulf