Jirgin ‘yan cirani ya kife a tekun Libiya

Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa aƙalla ‘yan cirani 6 sun mutu sakamakon nutsewa da kwale-kwalen da suke ciki ya yi a tashar ruwa ta Toruk da ke Libiya .

Makowanno biyu da suka gabata sama da mutane saba’in ne suka rasa rayukansu a Libiya bayan kwalekwalen da suke ciki ya kife.

Mafi yawan matafiyan waɗanda suke fitowa ne daga yankin nahiyar Afrika su tunkari Turai inda suke cewa suna tafiyar ne domin samun rayuwa mai inganci.

Ɗaruruwan matafiya ne ke ɗaukar wannan kasadar a kowacce shekara, inda wasunsu ke mutuwa a hanya saboda kifewar ababan hawar da suke kai.

Post masu alaƙa

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

Duk wanda ke da hannu a harin Amurka kan tsibirin Larak zai ɗanɗana kuɗarsa – Iran

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi