Garuruwan Da Ke Cikin Haɗarin Ambaliya Saboda Kogin Neja

Hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya ta yi gargaɗi kan barazanar aukuwar ambaliya sakamakon tumbatsar madatsun ruwa a wasu jihohin ƙasar.

Hukumar Nigeria Hydrological Services Agency (NiHsa ) ta yi kira ga jama’ar da ke zaune a wuraren da abin ka iya shafa da su gaggauta tashi daga wuraren kafin aukuwar ambaliyar da ake hasashe.

“Da yawa kogunanmu sun cika, kuma su ne ke bai wa madatusn ruwanmu ruwan. Abin ya kai ga su ma madatsun ruwan sun cika har sun fara sakin ruwan,” kamar yadda shugaban hukumar NiHsa Dr Umar Ibrahim ya shaida wa BBC.

Shugaban ya bayyana irin garuruwan da ke fuskantar barazanar ambaliyar, mafi yawansu a jihar Neja da Sokoto da Kebbi.

“Duk wani gari da ke kusa ko kuma kan hanyar Kogin Neja yana cikin barazana. Garuruwa kamar Bargu, Fatagi, Makwa – duka suna kan hanyar kogin da ke cikin jihar Neja.

“A ɓangaren Jaba kuma, akwai su Gungu, Gana, Bare, Goba, Baro – duk su ma suna cikin haɗari.”

Post masu alaƙa

An kashe kwamandojin ’yan bindiga biyu a Katsina

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

Nafi’u ya gargaɗi Atiku ya daina sukar Tinubu da sunan ADC