Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin garkuwa da mutane tare da ceto mutum 23

Sojojin Najeriya sun ce sun ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, tare da daƙile wani yunƙurin sace wasu mutane a yayin samamen da suka kai kan ƴanbiniga a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Post mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 5 ga watan Satumba.

Jami’in yaɗa labarai na rundunar Operation Fansan Yamma, Kanal Aliyu Danja, ya ce an gudanar da aikin ne a ƙananan hukumomin Anka da Bungudu.

Kanal Danja ya ce binciken farko ya nuna cewa ƴanbindigar sun yi garkuwa da mutanen ne daga ƙaramar hukumar Gummi, inda suka shafe kusan mako uku a hannunsu kafin a ceto su.

Ya ƙara da cewa mutanen da aka ceto suna samun kulawar likita da sauran tallafin da ya dace kafin a haɗa su da iyalansu.

Ya ƙara da cewa a ƙaramar hukumar Bungudu ne dakarun suka daƙile yunƙurin yin garkuwa da mutane bayan da wasu ƴanbindiga suka kai hari garin Dankurmi.

Post masu alaƙa

ADC ta fitar da sunayen ’yan takarar gwamnanta a jihohi 28

Sarkin Gumel Ahmed Muhammad Sani II ya rasu

NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi