Danjuma Goje ya yi fatali da maslaha a Gombe ta Tsakiya

Sanatan da ke wakiltar Gombe ta Tsakiya, Muhammad Danjuma Goje, ya yi fatali da tsarin maslaha da Jam’iyyar APC ta Jihar Gombe ta bi wajen tsayar da ’yan takara, yana mai cewa matakin ya saɓa da dokokin zaɓe da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Wannan na zuwa ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a ranar Lahadi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, inda aka ayyana tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda DCP, Mohammed Ahmadu Deba (mai ritaya), a matsayin ɗan takarar Sanatan Gombe ta Tsakiya ta hanyar maslaha.

Sai dai a wata sanarwa da mai taimaka masa, Barrista Sa’idu Mu’azu Kumo, ya fitar, Goje ya bayyana cewa ba a bi sahihin tsari ba wajen yanke wannan hukunci.

A cewarsa, dokar zaɓe ta ƙasa ta tanadi hanyoyi guda biyu ne kawai na fidda ’yan takara, ko dai zaɓen fid-da-gwani kai tsaye ko kuma ta hannun wakilai, yana mai jaddada cewa dole ne jam’iyya ta bi waɗannan hanyoyi domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Goje ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da taron, inda ya ce ba a gayyaci dukkan ’yan takarar da suka sayi fom ba, duk da cewa sun bi ka’ida wajen nuna sha’awarsu.

Ya ƙara da cewa abin da ya dace shi ne jam’iyyar ta shirya sahihin zaɓen fid-da- gwani da Hukumar Zabee ta Kasa (INEC) tare da jami’an tsaro za su sa ido a kai, domin tabbatar da sahihancin tsarin.

Sanatan ya gargaɗi cewa duk wani yunƙuri na tilasta ɗan takara ta hanyar maslaha ba tare da bin doka ba, barazana ce ga dimokuraɗiyya, yana mai kira ga jam’iyyar da ta gyara kuskuren da aka yi.

Lamarin dai na nuni da yiwuwar ɓarkewar sabani a cikin jam’iyyar APC a Gombe, yayin da ake tunkarar zaɓukan shekarar 2027.

Post masu alaƙa

Pantami zai je kotu bayan APC ta ba Jamilu Gwamna takarar Gwamnan Gombe

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM

Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba rancen naira miliyan dubu huɗu