Juyin mulki: Mutum 2 sun amince sun san da shirin kifar da gwamnati

Mutum biyu daga cikin mutane shida da ake tuhuma kan zargin yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun amince cewa sun shaida wa kotu cewa sun san da shirin, kamar yadda aka nuna a wasu bidiyoyi da aka gabatar a Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja suka nuna.

Bidiyon, waɗanda ke cikin wani kundin ajiya da masu gabatar da ƙara suka gabatar, ya ƙunshi tambayoyin da aka yi wa wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma, ciki har da tsohon Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya Erasmus Ochegobia Victor, da Sufeton ’Yan Sanda Ahmed Ibrahim, da kuma Manjo-Janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya.

A cikin bidiyon, Victor da Ibrahim sun amince cewa sun san da shirin juyin mulkin, amma ba su kai rahoto ba hukumomi, yayin da Gana ya bayyana cewa bai san komai game da shirin ba.

Victor ya bayyana cewa ya san wanda ake zargi da jagorantar shirin, wani Kanar ɗin soja mai aiki, kuma ya ce ya ji tattaunawa kan yadda za a kifar da gwamnati.
Ya ce an nemi ya taimaka da kuɗaɗe da kuma samar da wurin zama ga masu shirin, tare da alƙawarin ba shi muƙami idan suka yi nasara, amma ya ce ya ƙi shiga.

Sai dai ya amince cewa ya ci gaba da mu’amala da su ta hanyar wasu hanyoyin sadarwa na sirri, inda ake amfani da kalmomin sirri. Amma ya ce bai kai rahoton shirin ba saboda alaƙar da ke tsakaninsa da wanda ake zargi.

Shi kuma Ahmed Ibrahim, wanda ke aiki a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce da farko an tuntuɓe shi ne domin taimakawa wajen neman ƙarin girma ga jami’in, amma daga baya tattaunawar ta rikiɗe zuwa shirin kifar da gwamnati.

Ya amince cewa ya karɓi kuɗaɗe tsakanin Naira miliyan 1.4 zuwa 1.5, kuma ya taimaka wajen duba wasu wurare a kusa da Fadar Shugaban Ƙasa, ciki har da Aguda House, tare da ɗaukar hotuna da nazarin hanyoyin shiga.

Ya kuma tabbatar da cewa ana amfani da wasu kalmomi kamar “taki” da “noma” a matsayin sirri domin nufin kuɗaɗen da kuma shirin juyin mulkin.

Sai dai Gana ya musanta hannu a yunƙurin juyin mulkin, yana mai cewa tun bayan ritayarsa daga aikin soja a shekarar 2010 yana rayuwa cikin nutsuwa.

Ya ce duk da cewa ya san wanda ake zargi, amma bai san da wani shirin juyin mulki ba, kuma da ya sani da ya kai rahoto.

Amma ya amince cewa ya taɓa tura wa wasu saƙonni da suka shafi gwamnati a WhatsApp, amma ya ce ba shi ne ya ƙirƙire su ba.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta ɗage sauraron karar zuwa ranar Talata, 5 ga Mayu

Post masu alaƙa

NNPCL ya ƙulla yarjejeniyar gyara matatun man fetur na Warri da Fatakwal

Danjuma Goje ya yi fatali da maslaha a Gombe ta Tsakiya

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM