Babban sufeton ƴan sandan Nijeriya, Olatunji Rilwan Disu, ya yabawa dakarun rundunar ƴan sandan jihar Kano, bisa nasarorin da suka samu wajen yaƙi da masu aikata laifuka da murƙushe yunƙurin kutsowar ƴan bindiga tare da tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Olatunji Disu, wanda ya samu wakilcin muƙaddashin sufeton ƴan sandan Najeriya, DIG Sulaiman Muhammed Abdul, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki, da ya fara yi a jahohin arewa maso yammacin ƙasar domin duba yanayin tsaron yankin, inda ya buƙaci dakarun rundunar su ƙara zage damtse wajen yaƙi da masu aikata laifuka.
DIG Sulaiman Abdul, ya ce jihar Kano ita ce cibiyar kasuwancin Najeriya, domin zaman lafiyarta na yin naso zuwa wasu sassan jahohi dama ƙasa baki ɗaya.
Muƙaddashin sufeton ƴan sandan, ya jaddada muhimmancin amfani da bayanan sirri da kuma fasahar zamani ta ( AI) wajen gano masu aikata laifuka, ko masu tayar da zaune tsaye a cikin al’umma.
Ya buƙaci jami’an rundunar su ƙara ƙarfafa alaƙarsu da jama’a da shugabannin al’umma da malamai da matasa da kuma ’yan kasuwa domin samun sahihan bayanan da za su taimaka wajen hana aikata laifuka.
Ya ƙara da cewa babban sufeton ya fito da tsare-tsaren inganta walwalar jami’an ciki harda mallakar muhalli da kuma ƙarin girma ga jami’an ƴan sandan.
Haka kuma ya gargadi jami’an rundunar da su guji duk wani nau’in cin zarafi ɗan adam ko cin hanci ko yin amfani da Kakinsu ba bisa ka’ida ba, yana mai cewa irin waɗannan halaye na rage amincewar da jama’a ke yi wa jami’an tsaro.
Kwamishinan ya yabawa sarakunan gargajiya bisa haɗin kai da suke basu koda yaushe, sai dai ya buƙaci ƙarin haɗin kai daga kwamitin PCRC wajen ba su sashihan bayanan sirri da za su taimatawa tsaro.
Shugaban kwamitin PCRC na jihar Kano, Ambasada Ali Hassan T. Bayero, ya ce aikin tsaro na kowa ne ba iya jami’an tsaro ba, sai an haɗu baki ɗaya za a cimma nasara.
A ƙarshe, DIG Sulaiman Abdul, ya tabbatar da cewa rundunar ƴan sandan Najeriya za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin yaƙi da laifuka da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da cewa Jihar Kano ta ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da walwala.