’Yan Majalisar Wakilai tsagin ’yan adawa, sun nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da harkokin siyasar zaɓen 2027 tare da mayar da hankali kan matsalolin tsaro da tattalin arziƙi da suka addabi ƙasar nan.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Fred Agbedi, ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli masu tarin yawa da suka haɗa da garkuwa da mutane, kashe-kashe, talauci da tsadar rayuwa.
Ya zargi gwamnati da fifita siyasa a kan gudanar da mulki.
’Yan majalisar sun kafa misali da sace ɗalibai a jihohin Borno, Oyo da Kogi, tare da mutuwar tsohon Kakakin Hedikwatar Tsaro Manjo Janar Abubakar Rabe, a hannun ’yan bindiga.
Sun ce idan har tsohon babban jami’in soja ba shi da tsaro, to talakawan ƙasa za su fi kowa kasancewa cikin hatsari.
Tsagin ’yan adawar ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya dakatar da duk wani shiri na sake tsayawa takara a 2027, ya kuma ƙaddamar da shiri na watanni shida don inganta da tsaro da tattalin arziƙi.
Haka kuma sun nemi a ɗauki matakan gaggawa domin ceto ɗaliban da aka sace, bincike kan musababbin mutuwar Janar Rabe da kuma sake fasalin tsarin tsaron ƙasar.
Hakazalika, sun soki hukuncin kotu da ya umarci soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa guda biyar.