Rahotanni daga Jihar Neja na cewa aƙalla mutane 60 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata tanka ta kife a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wanda ke a Jihar Neja.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) shiyyar Neja, Kumar Tsukwam, ya ce akasarin waɗanda abin ya rutsa da su talakawa ne mazauna yankin da suka yi gaggawar ɗiban man da ya zube bayan motar ta kife.
“Mutane da yawa sun taru domin ɗiban mai duk da ƙoƙarin da aka yi na hana su.
“Kwatsam, sai tankar ta kama wuta, ta kuma kona wata motar dakon mai, ya zuwa yanzu an kwashe gawarwaki 60 da aka gano a wurin.”
Gwamnan jihar Neja Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa a sanarwar da sakataren watsa labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar.