Sakamakon wasu abubuwa marasa daɗi da suka auku a filayen tashi da saukar jiragen sama na baya-bayan nan, hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin cewa dukkan fasinjojin su kashe wayarsu a lokacin da suka shiga jirgin sama.
A wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, Darakta Janar na hukumar ta NCAA, Chris Najomo, ya ce dole ne fasinjoji su kashe duk wayoyi a lokacin da jirage ke sauka ko tashi a dukkan filayen jiragen saman Najeriya.
Umarnin da hukumar ta bayar ya biyo bayan ce-ce-ku-cen da aka yi a baya-bayan nan da ya shafi wata fasinja mai suna Comfort Emmanson, da ma’aikaciyar kamfanin jirgin sama na Ibom Air.
Shugaban hukumar ta NCAA ya ce hakan zai dakatar saɓanin da ake samu a ƙa’idojin kamfanonin jiragen sama, waɗanda suka haifar da ruɗani a tsakanin fasinjoji.
“A matsayin hanyar da za a bi don guje wa ruɗani, yanzu dole ne a kashe duk wayoyi da duk wasu na’urorin laturoni na tafi-da-gidanka a lokacin da jirgin ke sauka ko tashi a dukkan kamfanonin jiragen sama na Najeriya. A kashe wayar baki ɗaya, babu sauran batun tsarin kashe layi na ‘flight mode”, kamar yadda ya bayyana.
“Saboda haka ana buƙatar kamfanonin jiragen sama na Najeriya su yi gyara ga kundin tsarin aikinsu don tabbatar da wannan doka sannan su miƙa ga hukumar NCAA domin neman amincewa,” in ji shi