Fiye Da Rabin Mutanen Argentina Na Fama Da Talauci

Wani rahoto da Hukumar ƙididdiga ta ƙasar Argentina ta fitar  na nuni da cewa  rabin mutanen ƙasar  na fama da matsanancin Talauci.

Wannan na bayyana cewa an sami ƙaruwar talauci da kaso 40% cikin 100% na shekarar da ta gabata, kuma ya nuna tasirin matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatin  shugaban Ƙasar Javier Millei  ta ɓullo da su.

Tun bayan hawan Mista Javier a watan Disambar 2023, Gwamnati ta rage tallafin da ta ke bayarwa kan man fetur da sufuri da makamashi da sauransu.

Hauhawar farashin kayayyaki a Argentina a cikin watan Agusta  ya kasance ɗaya daga cikin mafi girma a duniya.

Post masu alaƙa

Kotu ta dage hukunci kan shari’ar datse yatsa bisa alkawarin naira miliyan 80.

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

Farashin mai ya ɗaga a duniya bayan soke tattaunawar Iran da ƙasashen Gulf