HISBAH Ta Gano Masu Ɗaukar Nauyin Yaɗa Bidiyon Tsiraici

Hukumar HISBAH ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa sun gano waɗan da suke ɗaukar nauyin yaɗa biyon tsiraici da ke tashe a ‘yan kwanakin nan,

Shugaban Hukumar a Jihar  Kano, Mallam Aminu Ibrahim Daurawa  ne ya bayyana hakan , inda yace a binciken da suka gudanar, sun gano cewa daga ƙasashen waje ake ɗaukar nauyin masu yin waɗannan bidiyo kuma su yaɗa shi a kafafen sada zumunta.

A satin da ya gabata ta ne dai ake zargin wata budurwa da sakin faifan bidiyon ta tsirara  har na tsawon mintuna uku, babu ko zani a jikin ta.

Bayyanar wannan bidiyo ya haifar da cece-kuce a tasakanin mabiya shafukan na sada zumunta.

Post masu alaƙa

Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

An Kama Masu Safarar Miyagun Ƙwayoyi 7 A Jigawa