Fulato: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Ƙasa Ta Rufe Ofisoshin Kananan Hukumomin Jihar 17

Sifeto Janar na ‘yan sandan kasa, Usman Alkali Baba, ya umarci kwamishinan ‘yan sandan Filato, CP Bartholomew N. Onyeka da ya rufe dukkan manyan ofisoshin kananan hukumomin jihar 17.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan Filato DSP Alfred Alabo, ya ce ,matakin ya zama dole biyo bayan zaman dar dar, kan yiwuwar barkewar rikici kan neman shugabancin kananan hukumomin, da kuma barazana ga rayuka, dukiya da kuma sauran ababen more rayuwa.

Rundunar ‘yan sandan ta yi gargadin cewa ba za ta  zuba idanu ta kyale bata gari su tayar da zaune tsaye ba, dan haka aka rufe baki dayan manyan ofisoshin kananan hukumomin jihar Filato 17.

Daga karshe kwamishinan, ya yabawa al’ummar jihar Filato bisa yadda suke ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai , inda ya bukaci jama’a su ci gaba da gudanar da sana’o’insu cikin kwannciyar hankali.

Post masu alaƙa

Ana fargabar mutum daya ya rasu, wasu biyar sun jikkata yayin da yan jagaliya suka tarwatsa magoya bayan NDC a jihar Delta. 

Rundunar yan sandan Kano ta kama kasurgumin dan Daba da ake zargi da garkuwa da Yaro mai shekaru 9

NOA ta taya kungiyar kwallon kafa ta mata ta yan kasa da shekaru 17 nasarar lashe gasar kofin duniya.