Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeriya ta Jihar Yobe ta bayyana neman wani fursuna ruwa a jallo bayan ya tsere daga wurin da aka yi hatsarin mota sa’ilin da ake jigilar fursunoni daga Potiskum zuwa Damaturu.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Abdullahi Adamu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya tabbatar da cewa fursunan ya tsere ne daga gidan gyaran halin na Potiskum.
Rahoton ya bayyana cewa tserewar nasa ya faru ne a ranar 13 ga watan Afrilu, lokacin da motar da ke jigilar fursunoni zuwa Damaturu ta yi hatsari a kan hanya.
Wannan lamari mai ban takaici ya faru ne yayin da ake kokarin ceto waɗanda hatsarin ya shafa, inda fursunan ya yi amfani da wannan damar ya tsere daga wurin.
An bayyana sunan fursunan a matsayin Dahiru Mohammed, mai shekara 30, ɗan ƙauyen Askiwari da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Tarmuwa. Lambarsa ta fursuna ita ce J/1539/24, kuma an fara tsare shi ne a ranar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2024.
Hukumar ta gargaɗi jama’a cewa Dahiru Mohammed mutum ne mai haɗari, don haka ya kamata a guji ƙulla kowace irin mu’amala da shi.
Sun kuma yi kira ga duk wanda yake da bayani game da inda yake, ko kuma wanda ya ga wani mutum mai shakku a kusa da wurin da hatsarin ya faru a kan hanyar Potiskum zuwa Damaturu, da ya hanzarta kai rahoto ga ofishin ’yan sanda ko gidan gyaran halin mafi kusa.