Gabatar Da Sabon Marubuci

Muna sanar da abokan hulɗar mu cewa Muhammad S. Ahmad Babban Jami’in Na’ura da ke Sashen Nazarin Labarin Ƙasa a Jami’ar Bayero ta Kano ya zama ɗaya daga cikin masu rubutun sharhi da fashin baki a wannan kafa.

Malam Muhammad S. Ahmad gogaggen marubuci ne a kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen Najeriya. Da ya jima ana yi da su a fagen sharhi akan al’amuran yau da kullum.

Da yardar Allah, za a rika wallafa sharhin Muhammad S. Ahmad akan al’amuran yau da kullum duk ranar Asabar.

Muna sanar da abokan hulɗar mu cewa za su iya tuntubar Muhammad S. Ahmad ya yi musu ƙarin haske dangane da wani rubutu da ya yi ko sharhi ta muhammadsahmad00@ gmail.com

 

 

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da garkuwa da mutane,sannan an kwato Drone.

Ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta buƙaci a biya diyyar masu haƙar ma’adinai 37 da suka rasu Neja

Atiku ya buƙaci Tinubu ya yi bayanin dalilinsa na ƙin halartar taron UNGA karo na uku a jere