Gidauniyar SURE 4 U ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya (Immigration) Muhammad Babandede, OFR, OCM, ta tallafawa iyayen marayu dubu ɗaya da ɗari shida da tamanin da tara (1689) a yankin Hadejia jihar Jigawa.
Iyayen marayun da aka zabo sun kai 220 kuma binciken da gidauniyar ta gudanar ta gano cewar suna da yara 1689 a ƙarƙashinsu, waɗanda ɗari bakwai da huɗu (704) ne kacal ke zuwa makaranta yayin da sauran ɗari tara da tamanin da huɗu (984) basa zuwa makaranta.
Daga yake gabatar da jawabinsa wanda ya samar da gidauniyar SURE 4U , tsohon shugaban Hukumar Shigi da Fici ta Najeriya (Immigration) Muhammad Babandede, OFR, OCM, ya bayyana cewa sun bayar da tallafin saboda Allah, domin dukkan wadanda suka amfana basu san su ba.
Muhammad Babandede, ya kuma yi kira ga matan da suka amfana da tallafin su yi amfani dashi yadda yakamata don inganta rayuwarsu da kuma yayansu bisa halin rashi da suke ciki.
A cewarsa kafin ya aiwatar da shirin sai da ya gayyato yan siyasa don su sanya hannun a ciki, kuma sun yi amfani da masu unguwanni da kungiyoyi masu zaman kansu wajen tantancewar.
Haka zalika ya bayyana wa shugaban majalissar sarakunan jihar jigawa, mai martaba sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje con, sun samu yara 984 da basa zuwa makaranta kuma sun yi alkawarin mayar da su makarantu , sannan yara 705 da suke zuwa makaranta za a dauki nauyin karatunsu.
Muhammad Babandede, ya ce duk da abun ya bukatar kudi sun kiyasta zai lakume sama da naira miliyan hamsin, domin a yanzu haka akwai wadanda suke biya wa kudin makaranta.
- Yan Sanda Sun Kubutar Mutane 3 Daga Hannun Masu Garkuwa A Jahohin Kano Da Kaduna
- Kotu Ta Dage Shari’ar Kisan Gillar Da Aka Yiwa Matar Aure A Unguwar Farawa Kano
Ko-odinetan SURE 4U, Munnir Yari, ya ce sun ba wa ko wace uwar marayu buhun shinkafa mai nauyin 25kg da man gyada da Sukari, da Atamfa da Naira dubu Ashirin-ashirin, tare da kira agare su kar su siyar da kayan abinci domin kuma marayun kara mayar da hankali kan karatunsu.
Sai dai ya bukaci masu hannu da shuni da su fara taimakawa makotansu a matsayin wata hanya ta farko.
Yayin taron, Sanata mai wakiltar Jigawa ta Gabas Sanata Abdulhamid Malam Madori , ya bai wa iyayen marayun tallafin Naira dubu goma-goma su yi kuɗin mota.
Anasa jawabin mai martaba sarkin Hadejia, Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje con, shugaban majalissar sarakunan jihar Jigawa, ya godewa gidauniyar sure 4U bisa wannan tallafi data kawo masarautar Hadejia.
Sarkin ya bukaci jama’a su kasance masu taimakawa juna, domin hakan yana kawo hadin kai da ci gaba mai dorewa.
Wadanda suka amfani da tallafin sun bayyana farin cikinsu tare da yin godiya ga gidauniyar SURE 4U data tallafa musu, inda suka addu’ar Allah ya kara bunkasa ta.
Taron ya samu halattar masu rike da masarautun gargajiya, wakilan gwamnatin Jigawa, yan siyasa da kuma Ambasada Haruna Ginsau, wanda gidauniyar SURE 4U ta nada shi a matsayin ambasadanta .