Gobara Ta Yi Barna A Bunkure Jihar Kano

Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida.

Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, ya ce, mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar.

Bayan haka, an kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa.

Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin, inda suka bayyana cewa gobarar ta lalata gidaje guda shida, kaya, hatsi, dabbobi da kuma wasu kayayyakin amfanin yau da kullum da darajarsu ta kai ta miliyoyin Naira.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne sakamakon wuta da aka yi amfani da ita wajen dafa abinci, amma aka bar ta ba tare da an kashe ba.

Sarkin ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa kuma ya ba su tallafin Naira 200,000 domin rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

Post masu alaƙa

Kotu ta yankewa Mustapha Usha hukuncin kisa kan kashe matashi a unguwar Bambazau

Kotu ta daure Saminu shekaru 15 kan kisan abokin kasuwancinsa, ta umarce shi da biyan Naira miliyan 10.

Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da yin barazanar garkuwa da Dagacin garin Bangare a Kano.