Daga Ali Rabiu Ali, Dutse.
Gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi ya ƙaddamar da wani kwamati daga cikin majalisar zartarwar Jihar da zai kula da harkokin abinci mai gina jiki da ake wa laƙabi da “nutrition 774”.
Namadi ya Jaddada aniyar sa ta daƙile matsalar tamowa da kuma inganta samar da abinci a fadin Jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Juma’a 24 ga watan Oktoba, 2025 a yayin da ya karbi bakuncin babbar mai bai wa shugaban ƙasa shawara akan harkokin lafiyar al’umma Misis. Uju Rochas-Anwuka, da ke ofishin mataimakin shugaban ƙasa domin kaddamar da shirin samar da abinci mai gina cijiki wato nutrition 774.
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas
- An cire Najeriya Daga Jerin Kasashe Na FATF Masu Halasta Kuɗin Haram
Da take Jawabi Misis. Uju Rochas-Anwuka, ta ce tazo Jigawa ne da izinin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima domin tattaunawa da gwamana da muƙarraban sa akan al’amarin da ya shafi cutar tamowa da ke kawo tarnaki ga lafiyar yara.
Ta ce shirin nutrition 774 Wanda ke ɗaya daga cikin shirin tsarin canza rayuwa na shugaban ƙasa wato renewed Nigerian na ofishin mataimakin shugaban kasa Wanda aka sa shi a cikin shirin majalisar kasa na tabbatar da samuwar abinci mai gina jiki domin dakile cutar yunwa da makamancin hakan a fadin Najeriya.
Misis. Anwuka ta ce cutar yunwa ba kawai matsalar rashin lafiya bace har ma da tsarin tattalin arzikin kasa.
Da ya ke maida jawabi, gwaman Malam Umar Namadi ya nuna farin cikin sa ga ofishin mataimakin shugaban ƙasa wurin samar da wannan tsarin in da ya ce Jihar Jigawa na kan gaba wajen samar da tsari mai kyau a fannin abinci mai gina jiki a fanoni da dama. In da ya jaddada cewa ayyukan abinci mai inganci na buƙatar shiga cikin al’umma da kuma sa hannun su.
Gwamnan daga bisani ya bayyana shirin masaki wanda gwamnatin Jihar ta kirkira tun a shekarar 2020 domin koyawa mata yadda za su yi abinci mai gina jiki a matsayin babban shirin da ya yi tasiri wajen daƙile cutar tamowa da kaso mai tsoka a fadin jihar Jigawa.
Gwamna Namadi ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da wani muhimmin shiri na tom brown da aka horar da mata 600 a ƙanan hukumomin jihar 27 domin samar da abinci mai gina jiki.
Daga bisani Namadi ya ce gwamnatin jihar Jigawa na bayar da nai miliyan 250 yayin da Yanmajalisun jihar ke bada naira miliyan 300 domin siyan gyadar tamowa wacca ake Kira da (RUTF) domin rabawa yaran da ke dauke da cutar tamowa don samun lafiya.
Malam Umar Namadi ya ce jihar Jigawa za ta zama ta farko da za ta cimma kudurin nutrition 774 a fadin Najeriya.

