Gwamna Zulum ya ce sun rufe kasuwar Jilli

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce gwamnatin jihar Bornon ta rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka gabata kasancewarta matattarar ƴan ta’adda.

Gwamnan wanda ya faɗi hakan a wata sanarwa da yake mayar da martani ga harin ’kuskure” da sojojin saman Najeriya suka musanta wanda bayanai suka nuna mutum fiye da 50 sun mutu, ranar Asabar.

“An sanar da ni kan abin da ya aru dangane da harin sama da rundunar sojin sama ta kai a kasuwar Jilli da ke kan iyakar Borno da Yobe. Ina son sanar da cewa gwamnatin Borno ta rufe kasuwar Jilli da Gazabure shekaru biyar da suka wuce.”

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai