Za mu baiwa sojojinmu wadatattu makamai don yaƙi da ‘yan ta’adda -Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta shirya domin ƙarfafa sojojin Najeriya da ke yaƙi da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a faɗin ƙasar.

Ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar kwana guda da ya kai jihar Bayelsa a ranar Juma’a, inda ya ƙaddamar da wani aiki da Gwamna Douye Diri ya yi, inda shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da baiwa dakarunta atisaye da kayan aiki domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar.

Ya jaddada cewa sun mayar da hankali wajen neman cin nasara da kawo ƙarshen duk wasu lamuran tsaro.

Rahotanni sun ambato tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan da mai ɗakinsa Patience na cikin waɗanda suka raka shugaban ƙasar taron.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai