Gwamnan Jihar Kano Ya Yi Wa Wasu Fursunoni 12 Afuwa

A jiya ne Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa wasu fursunoni 12 da aka tabbatar wa hukuncin kisa afuwa.

Kuma wadanda bayanai ke nuna cewa tuni aka zartar wa da shida daga cikinsu hukuncin daurin rai da rai.

Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Yari reshen Jihar Kano, SC Musbahu Lawan Nassarawa ya fitar.

Sai cece-kuce ya biyo bayan wannan sanarwa inda wasu suke ƙalubalantar gwamnatin Kano a kan wannan hukunci.

jam`iyyar adawa ta NNPP, ita ma ta yi zargin cewa Gwamnan ya yi wa fursunonin afuwa ne don gwamnatinsa ta yi amfani da su wajen haddasa yamutsi a lokacin zaben gwamnan da za a yi a karshen mako nan, saboda a cewarsu, Jam’iyyar ta APC ba za ta kai labari ba.

Kamar yadda  magana da yawun ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar NNPP, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana.

Sai dai gwamnatin Kanon ta bakin kwamishinan yada labaranta, Mallam Muhammad Garba ta musanta wannan zargin, tana cewa NNPP ce dai ta karaya ta fara neman dalili ko abin fada bayan ta sha kaye a zaben gwamna da ke tafe.

Ya kuma kara da cewa babu yadda za a yi mutane 12 kacal su je kananan hukumomi masu yawa da ake da su a Kano domin ta da zaune tsaye.

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr