INEC Ta dage zaɓen gwamnoni da’Yan Majalisun Jihohi a Najeriya

Hukumar Zaɓe ta Najeriya INEC ta ɗage zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihohi da mako guda, wato zuwa 18 ga watan Maris ɗin shekarar da muke ciki.

INEC ta tabbatar da hakane a wani takarda na ɗage zaɓen, bayan wani taron gaggawa da manyan jami’an hukumar suka yi a dare jiya laraba a Abuja.

Kafofin yaɗa labarai na Najeriya sun ambato cewa INEC ba ta kammala saita ‘tantance masu zaɓe ba ta BVAS wadda aka yi amfani da ita a zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabirairu.

Sun ƙara da cewa hukumar ta ce sai ta samu damar kwashe bayananta da ta tattara na a yayin zaɓen shugaban ƙasar zuwa wani rumbunta na daban kafin ta sake saita na’urar ta yadda za a yi zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ba tare da wata damuwa ba.

Tun da farko, an tsara gudanar da zaɓen ne a ranar asabar 11 ga watan Maris.

Post masu alaƙa

Babandede Ya Ziyarci Iyalan Hon. Laushi, Ya Ba Su Tallafi

Da Fulani Aka Kama da Wuraren ƙera Makamai a Filato, da War Haka Duniya ta Dauka:-Zagazola Makama

Gwamna Bala Mohammed ya canja sheka daga jam’iyar PDP zuwa jam’iyyar APM