Da yake jawabi yayin buɗe Asibitin, Gwamna Abba Kabir ya zargi gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje da sayar da Asibitin, lamarin da ya jefa al’ummar jihar cikin wahala.
A cewar sa, hakan ta sanya ya ci alwashin idan ya zama gwamnan Kano sai ya ƙwato wa al’ummar Kanon kayansu.
A cewar Gwamnan “Duk da irin roƙon da al’umma suka riƙa yi, amma gwamnatin da ta gabata ta sayar da wannan asibiti.
Hakan ya sanya al’umma suka rika shan wahala. Dole suka riƙa zuwa neman Asibitocin yara masu tsada kuma ba lallai suna da ingancin wannan ba.
Ya ƙara da cewa “Da suka ga haka, sai suka sha alwashin kwato wa al’umma asibitinsu.
Abba Kabir ya ce, yau ga shi sun cika alƙawari. Suna cikin farin ciki da alfahari da wannan gagarumin aikin.
Ya ce asibitin yana ɗauke da gadaje 86, kuma an saka masa kayayyakin aiki na zamani da za a rika kula da lafiya cikin inganci da sauƙi.
Ya kuma ja kunnen jami’an lafiya na Asibitin da su kula da gudanar da ayyukansu, ya gargaɗe su a kan yin fashi da makara, inda ya ce “gwamnati ba za ta lamunci sakaci da aiki ba.”
A nasa jawabin, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gode wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ƙoƙarin da ya yi na sake buɗe Asibitin.