Gwamnan Jihar Neja Ya Sauke Shugaban Hukumar Zabe Na Jihar

Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago  ya sauke shuwagabannin hukuman zaɓe mai zaman kanta ta jihar.

Sakataren gwamnatin jihar ta Neja, Alhaji Abubakar Usman ne ya bayyana hakan a garin Minna a jiya.

Hukuncin sauke jami’an ta fara aiki ne tun a ranar 29 ga watan Mayun da ta gabata.

Inda ya bayyana cewa ana umartar jami’an hukumar da su miƙa duk wani kaya mallakin jihar ga manyan daraktoci a hukumar.

Haka kuma kanfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa ko da a ranar 27 ga watan Satumbar 2022, sai da majalisar dokoki ta jihar ta sallami shugaban hukumar zaɓen ta jihar, Alhaji Baba Aminu, kan zargin yin almundahana.

Amma sai ruwa tasha. Sai a yanzu da sabuwar gwamnati ta kama aiki wacce ta tabbatar da sallamar tasa.

Related posts

Ba Daidai Ba Ne Tinubu Ya Ci Gaba Da Ciyo Bashi Duk Da Cire Tallafin Mai – Sanusi

Yan Sanda Dubu 45,000 Ne Za Su Kula Da Zaben Jihar Anambra

Amurka Ta Soke Bizar Wole Soyinka