Gwamnan jihar Zamfara ya rage yawan ma’aikatun jihar daga 28 zuwa 16

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaba hannu kan rage ma’aikatun gwamnatin jihar daga 28 zuwa 16, don Farfado da tattalin arzikin Jihar.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa da aka fitar ta hannun mai magana da yawun gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris.

Sabbin ma’aikatun da aka amince da su sun hada da ma’aikatar Noma, Kasafin Kudi da Kimiyya da Fasaha, Muhalli da Albarkatun Kasa, Kudi, Lafiya da Kasuwanci da kuma Ciniki da Masana’antu,

Sauran su ne Ma’aikatar Watsa Labarai da Gidaje da Raya Birane da Ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu sai ma’aikatar Al’amuran Addini da Ma’aikatar Harkokin Mata da ta Ayyuka da kuma ma’aikatar Matasa da Wasanni da ta Tsaron Cikin Gida.

Post masu alaƙa

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP