Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da nadin cif-joji mace ta farko a tarihin Kano

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta tabbatar da mai shari’a Dije Aboki a matsayin cif joji ta jihar Kano.

Wannan naɗi nata ya biyo bayan aikewa da sunanta da gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi a cikin wata wasika ga majalisar dokokin jihar Kano wanda shugaban majalisar, Ismail Falgore, ya karanta ta a gaban majalisar a jiya.

Wannan ke nufi da kasancewar mai shari’a Dije Aboki a matsayin mace da ta zama cikakkiyar cif joji ta farko a tarihin jihar Kano.

Tun a baya dai, tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ayyana ta a matsayin mukaddashin cif joji a watan Maris ta jiha, sai dai a yanzu ta zama cikakkiyar cif jojin.

Post masu alaƙa

Ba za mu dawo da tallafin man fetur ba —Fadar Shugaban Ƙasa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP