Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Sake Wasu Sabbin Naɗe-naɗe Guda 5

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da naɗa wasu ƙarin mutane biyar mukamai daban-daban.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu

Wadanda aka naɗa sun haɗa da:

1. Engr. Garba Ahmed Bichi
Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano

2. Dr. Rahila Mukhtar
Sakatariyar Hukumar Kula da Taimakekeniya Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA).

3. Hassan Baba Danbaffa

Daraktan Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano (KARMA).

4. Arc. Ibrahim Yakubu
Daraktan Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA).

5. Abdulkadir Abdussalam
Akanta Janar na Jihar Kano

Sanarwar ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da lokacin da za’a rantsar da wadanda aka nada domin ba su damar sauke nauyin da aka dora musu nan take.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro