Koriya ta Arewa Ta Harba Makamin Leƙen Asirin da ya Sanya Wa Ƙasashe 2 Fargaba

Ƙoƙarin ƙasar Koriya ta Arewa na  harba makami mai linzami da ke ɗauke da tauraron dan’Adam na leken asiri ya gamu da tazgaro, Lamarin ya sa Japan da Koriya ta Kudu umartar miliyoyin mutane su shirya sauya matsugunai.

Kakakin gwamnatin Japan ya ce, gargadin ya fito fili ne bayan tabbatar da cewa makamin ya fada a wani yanki na daban.

 Kafar yada labarai ta gwamnatin Pyongyang ta ce, makamin ya fada a cikin teku saboda matsalar da suka samu. Sannan sun ce za su sake aiwatar da wannan gwaji nan ba da jimawa ba.

Amurka ta bi sahun Japan da Koriya ta Kudu wajen Alla-wadarai da wannan gwaji, tana mai cewa yana dauke da makamin da ya saɓawa dokokin Majalisar Dinkin Duniya.

Post masu alaƙa

Yan sanda da INEC sun yaba da yadda zaɓen Dawakin Kudu ke gudana a Kano.

An dakatar da shugaban NSCDC a Neja kan mutuwar masu haƙar ma’adanai 37

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta raba wa iyalan jami’anta 62 sama da Naira miliyan 34