Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya rantsar da karin kwamishinoni 3

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci taron majalisar zartarwa na jihar a jiya Litinin, Inda a yayin taron aka rantsar da sabbin kwamishinoni guda 3

Sabbin kwamishinonin da aka rantsar sun haɗar da:

1- Hajiya Amina S. Abdullahi (HOD) a matsayin kwamisiniyar ma’aikatar ayyuka na musamman.

2. Hon. Ibrahim Namadi Dala Kwamishinan Ma’aikatar Duba Ayyuka da Nagartar Aiki.

3. Prof. Ibrahim Jibrin Fagge a matsayin kwamishinan ma’aikatar kuɗi.

Yayin bikin rantsuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya sabbin kwamishinonin murna tare da horar su da su yi aiki bisa gaskiya da rikon amana.

Post masu alaƙa

Za a miƙa ƴan Najeriya da ake zargi damfara zuwa Amurka

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.