Gwamnati Ta Fitar Da Sunan Mutum 48 Da Ake Zargi Da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Najeriya

Gwamnatin Tarayya, ta fitar da sunan mutane da ƙungiyoyi 48 waɗanda ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a faɗin Najeriya.

Hukumar da ke sanya takunkumi ta Najeriya (Nigeria Sanctions Committee) ce, ta bayyana jerin sunayen a ranar Asabar, 11 ga watan Afrilu, 2026.

Sunayen ya ƙunshi ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin da bincike ya nuna suna da alaƙa da ayyukan tada ƙayar baya.

Daga cikin waɗanda aka ga sunansu har da mambobin ƙungiyoyi irin su IPOB, Ansaru, da kuma ƙungiyar ISWAP.

Wasu daga cikin fitattun mutane da sunansu ya bayyana cikin jerin, sun haɗa da Simon Ekpa da Tukur Mamu.

Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa wannan matakin na ɗaya daga cikin ƙoƙarinta na gano tare da toshe hanyoyin da ake bi wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Hakazalika, Gwamnatin ta bayar da umarnin rufe asusun bankunan waɗanda cikin jerin sunayen da aka fitar.

Ga sunayensu cikin hotuna a ƙasa:

Post masu alaƙa

PDP ce za ta lashe zaɓen 2027 a Jigawa — Sule Lamido

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .