Ko Amupitan ya sauka ko mu ɗauki matakin ban mamaki – ADC

Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya tace ko Shugaban Hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta INEC Joash Amupitan ya sauka daga muƙaminsa ko kuma sau ɗauki matakin da zai girgiza kasar.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne lokacin da take gabatar da wasu sabbin zarge-zarge kan shugaban hukumar.

ADC ta soki Amupitan kan tsofaffin bayanansa da ya wallafa a shafinsa na Twitter waɗanda suka riƙa nuna goyon bayansa ga jam’iyyar APC mai mulki.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar INEC ta hannun sakataren watsa labaranta Adedayo Oketola, tace Shugaban ya gargaɗi mutane da amfani da intanet wajen bata suna da kuma aikata laifuka ta internet da kuma amfani da bayanan bogi da yaɗa labaran ƙarya.

Ya kuma jaddada cewa INEC ƙarƙashin shugabanci Amupitan na fatan gudanar da zaɓe mai sahihanci da babu cutarwa cikinsa, inda ya shawarci mutane su riƙa neman bayanai daga kafar INEC kawai don gujewa bayanan ƙarya.

Da yake nasa bayanin kakakin ADC Bolaji Abdullahi ya ce, “Bayanan da aka samu na yadda shugaban INEC ke goyon bayan Bola Tinubu ba kawai ta da hanakali suke yi ba kawai, wata fitina ce da ke tunkarar tsarin zaɓen Najeriya.

“Dole ne Farfesa ya yi murabus, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba. Gaza hakan cin fuska ne ga mutanen Najeriya kuma haɗari ne ga dimokradiyyarta,” in ji Bolaji.

Post masu alaƙa

Ƴan bindiga sun sace tsohon mai magana da yawun soji a Katsina

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta rushe tsagin APC mai goyon bayan Wike a Ribas

Sojojin Najeriya sun ceto mutum 31 da aka sace a Zamfara