Wata Kotun Tarayya da ke Kalaba, Jihar Kuros Riba, ta yanke hukuncin daurin shekara biyu ga wata mata kan laifin safarar yara zuwa ƙasashen waje.
Kotun ta tura matar mai suna Asuquo Edem zuwa gidan gyaran hali na tsawon shekara biyu, tare da zaɓi na biyan tara.
Hukumar da ke yaƙi da fataucin bil’adama (NAPTIP) ce ta gurfanar da Asuquo Edem a gaban kotu.
A yayin yanke hukunci, mai shari’a Rosemary Dugbo Oghoghorie ta bayyana cewa kotu ta samu wacce ake tuhuma da laifi bisa tanadin doka.
An tabbatar da cewa Mbika Asuquo Edem ta aikata laifin safarar yara da kuma sayar da jariri kan kuɗi Naira dubu ɗari biyu.
NAPTIP ta gabatar da shaidar Mercy Aniekan Ekanem, wadda ta haifi jaririn da aka sayar. An tabbatar da cewa wasu mutane sun biya kuɗi, suka karɓi jaririn, sannan suka tafi da shi.
Rahotanni sun nuna cewa masu safarar yara kan sayar da jariran maza ko mata ga ma’auratan da ba su da haihuwa.
Suna sayar da jaririn namiji kan kuɗi naira dubu ɗari biyu, yayin da mace ake sayar da ita kan Naira dubu ɗari uku.