Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai

Hukumar Kula da Ingancin Ilimi da Jarabawa ta Jihar Binuwai (BEQAEB), ta rufe makarantun Orenda da Opal bisa zargin tilasta wa iyaye saya wa ’ya’yansu littattafai a makarantun.

Sakataren zartarwa na hukumar, Doktq Terna Francis ne, ya bayyana hakan a ranar Juma’a.

Ya ce matakin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da iyaye suka shigar kan karya dokar gwamnatin jihar da ta ba su damar sake amfani da tsofaffin littattafai ko sayen sababbi a duk inda suke so.

Francis, ya ce wasu ɗaliban da iyayensu ba su da kuɗin sayen littattafan da makarantun ke sayarwa, wanda hakan ya kai ga hukunta su ta hanyar ƙin duba aikin da aka ba su.

Ya ƙara da cewa mahukuntan makarantun sun ƙi amincewa ɗalibai su yi amfani da littattafan da iyayensu suka saya a wasu wurare.

A cewar Francis, hukumar ta gayyaci masu makarantun da shugabanninsu domin tattauna ƙorafe-ƙorafen, amma ba su halarci taron ba.

Daga nan ne hukumar ta nemi izinin kotu, wadda ta bayar da umarnin rufe makarantun.

Ya kuma zargi mai makarantun, Onyinye Okoye, da wasu ma’aikata da cin mutuncin jami’an hukumar da kuma lalata motar hukuma yayin da suke rufe makarantun.

Francis, ya ce makarantun za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai mamallakansu sun cika sharuɗan hukumar tare da bin dokokin gwamnatin jihar.

Ya buƙaci iyaye da ’ya’yansu suka fuskanci irin wannan cin zarafi da su shigar da ƙorafi a hukumance ga hukumar domin gudanar da bincike.

Post masu alaƙa

Sarkin Musulmi ya buƙaci masarautu suke rubuta tarihinsu

Yan sandan Kano sun gaiyaci Aminu Warkal kan zargin nuna bindiga.

2027: Sama da mutum 10,000 sun nuna goyon bayansu ga Tinubu da Namadi a mazabar Limawa