Wasu Mutum huɗu, ciki har da mai ciki mota ta hallaka yayin rakiyar gawar tsohon mataimakin shugaban ƙasar Malawi, Saulus Chilima.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Malawi, Saulus Chilima dai ya rasa ransa ne a wani hatsarin jirgi da rutsa da shi a makon Jiya.
Waɗanda suka shaida faruwar lamarin sun ce motar ta ƙwace ne inda ta bi ta kan mutanen.
Kawo yanzu dai, shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa akwai mutum 12 da suka jikkata sanadiyyar hatsarin da ya faru a daren ranar Lahadi.
Lamarin ya faru ne akan hanyar ƙauyen tsohon mataimakin shugaban kasar daga Lilongwe, babban birnin ƙasar Malawi.
An yi jana’izar Saulus Chilima a jiya Litinin a kauyensu da ke gundumar Ntcheu, mai nisan kilomita 180 daga kudancin babban birnin ƙasar.