Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kafa sabuwar Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Jihar domin inganta harkar wuta a jihar.
Majalisar Dokokin Jihar Gombe, ta amince da naɗe-naɗen shugaba da kwamishinonin hukumar, kuma za su fara aiki daga ranar 21 ga watan Janairu, 2026.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnati, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya ce kafa hukumar zai taimaka wajen kawo tsari mai kyau da kuma jawo masu zuba jari a ɓangaren wutar lantark
Ya ƙara da cewa an kafa hukumar ne domin inganta samar da wuta, da bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar shiga harkar samar da rarraba wuta.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Dakta Usman Abba Arabi a matsayin shugaba, Injiniya Sule Usman a matsayin kwamishinan fasaha, Abubakar Sa’ad a matsayin kwamishinan tattalin arziƙi, da Injiniya Ahmed Ibrahim Pindiga a matsayin kwamishinan wutar karkara.
Sauran sun haɗa da Lydia Ali a matsayin kwamishiniyar kuɗi da gudanarwa, da Talatu Abubakar a matsayin kwamishiniyar shari’a da bayar da lasisi.
Gwamna Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa yana da yaƙinin sabbin jami’an za su kawo sauyi a ɓangaren wutar lantarki a jihar.
Ya ce hukumar za ta taimaka wajen kare haƙƙin masu amfani da wuta, da kuma jawo sabbin masu zuba jari a birane da karkara.
Haka kuma, ya ce samar da ingantacciyar wuta yana da muhimmanci wajen bunƙasa masana’antu da tattalin arziƙi, musamman a yankunan da ke fama da ƙarancin wuta.
Masu sharhi na ganin cewa kafa wannan hukuma zai taimaka wajen magance matsalar rashin wuta da kuma bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Gombe.