Fargaba ta mamaye jihar Katsina yayin da ‘yan bindiga suka bukaci a ba su shanu dari bakwai (700) da tumaki dubu (1,000) daga wasu al’umma, tare da bayar da wa’adin kwanaki shida, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankunan tserewa
Mazauna wasu kauyuka a Karamar Hukumar Kankia ta Jihar Katsina sun shiga cikin tsananin firgici bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun bayar da wa’adin kwanaki shida suna neman shanu 700 da tumaki 1,000.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an isar da sakon ne ta hanyar wata takarda da aka kai wa kauyukan da abin ya shafa a ranar Alhamis, lamarin da ya sa mutane da dama suka tsere daga gidajensu saboda tsoron hare-hare masu zuwa.
Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida a ranar Asabar cewa wannan wa’adi ya biyo bayan watanni na cin zarafi da sace-sace da ake zargin kungiyoyin yan fashin daji na aikatawa a yankin.
A cewarsa, wani shahararren shugaban ‘yan bindiga ya taba kwashe dimbin dabbobin da aka sace bayan samun sabani da abokan aikinsa, kafin daga bisani ya nemi abin da ya kira “haraji” daga al’ummomin yankin.
Ya ce: “Akwai wani mai suna Muhammadu a cikin ‘yan bindigar wanda, bayan ya samu sabani da abokan aikinsa, ya zo da kimanin babura 200 ya kuma kwashe kusan dabbobi 1,700 da ya tara, yana zaune da su a garin Rimaye.”
To sai dai daraktan yada labaran gwamnatin jihar, Maiwada Danmalla, ya ce hukumomin tsaro na cigaba da sa ido kan lamarin, ya kara da cewa wasikar da aka aikewa mazauna yankunan watakila an yi hakan ne don razana jama’a.