Hukumar wayar da kai ta ƙasa NOA tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa NAWOJ, sun jaddada aniyarsu na ci gaba da ilimantar da mutane don inganta kyawawan ɗabi’u, da sanya kishin ƙasa, gabanin zaɓen 2027.
Babban Daraktan NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan inda ya ce wannan haɗin gwiwar na da muhimmanci wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da wayar da kan matasa, musamman ta hanyoyin sadarwar zamani.
Ya bayyana cewa hukumar na aiwatar da shirye-shirye kamar Nigerian Identity Project da kuma dawo da darasin Ilimin Ɗan ƙasa a makarantu domin inganta ƙishin ƙasa.
A nata ɓangaren, Shugabar ƙungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa, NAWOJ, Aishatu Ibrahim, ta ce sun kai ziyarar ce domin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen wayar da kan jama’a kan zaɓe musamman wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya a kafafen yaɗa labarai da na sada zumnunta.
Haka kuma, ɗaya daga cikin mambobin kwamitin amintattu na NAWOJ, Zubair Jide Atta, ya jaddada muhimmancin ɗabi’u da wayar da kan jama’a tare da ba da shawarar ƙara ilimin amfani da kafafen yada labarai a makarantu.
Daraktan yada Labaran hukumar NOA, Bala Musa, ya ce ɓangarorin biyu sun amince da ƙarfafa haɗin gwiwa don kawo mafita mai kyau da ci gaban Nijeriya.