Ƴar wasan kwallon kafa ta Najeriya, Asisat Oshoala ta ce ta san mahaifinta bai ji daɗin irin murnar da ta yi ba bayan cin kwallo a wasan da Najeriya ta doke Australia da ci 3-2.
Ƴar wasan Najeriyar ta bayyana haka ne a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram.
Oshoala ce dai ta zura kwallo na uku a wasansu da Australiya a Gasar Kofin Duniya ta Mata ranar Alhamis.
Inda Ta cire rigarta a lokacin da take murnar kwallon da ta ci.
Tun daga lokacin salon murnar da ta yi, ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masoya kwallon kafa a ciki da wajen ƙasar.
Yayin da mutane da yawa ke ganin babu wata matsala game da salon murnar, wasu kuma sun fusata da hakan.