Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da sanyin safiyar yau ɗin nan ya fara rusa wasu gine-gine a filayen gwamnati da ake zargin gwamnatin baya da cefanar da su.
A yayin wan nan rusau an rusa wani gini mai hawa uku da ke dɗauke da shaguna 90 da ke filin Sukuwar dawaki a cikin unguwar Nasarawa GRA a nan cikin birnin Kano.
Gwamnan wanda ya jagoranci aikin rusa ginin ya samu rakiyar kwamishinan ‘yan sanda Jihar, CP Muhammed Gumel.
Idan za’aiya tunawa, jim kadan bayan an rantsar da shi matsayin zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar ruguza gine-gine a jihar kan kadarorin gwamnati da aka cefanar da su ga Jama’a.