Gwamnatin jihar Kano tasha alwashin magance matsalar ruwan sha.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, yasha alwashin kawo ƙarshen matsalar ruwan sha, a yayin wata ziyarar gani da ido da yakai matatar ruwa ta Tamburawa dake jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Mustapha Muhammad, ya fitar.
A yayin rangadin, an gano matsaloli da suka haɗa da zubewar ruwa a bututu, lalacewar wasu injuna da kuma tsufan wasu kayayyaki, inda gwamnan ya yi alƙawarin daukar matakan gyara da sabunta wasu.
Da yake zantawa da manema labarai, Gwamna Abba ya jaddada ƙudurin gwamnatin sa na gyara cibiyoyin tace ruwa da inganta samar da ruwa ga al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na cewa gwamnati za ta haɗa kai da kwararru daga kasar China domin tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta kuma wadatacce, yana mai cewa samar da ruwa mai kyau na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Post masu alaƙa

Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar ADC

Babu wata kotu da ta wanke Murtala Sule Garko daga zargin badaƙalar kudi – Baba Jibo

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta raba Naira miliyan ɗaya ga matasa 36 a shirin haɗin gwiwa na magance aikata laifuka