Gwamnatin Kano ta daukaka ƙara kan hukuncin kotu kan rushe shaguna

Gwamnatin jihar Kano ta daukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke cewa ta biya diyyar Naira Miliyan Dubu 30 ga wadanda ta rushewa shaguna a filin idi dake unguwar kofar mata.

Kotun ta yanke hukuncin biyan diyyar Naira Miliyan Dubu 30 din ne ga ‘yan kasuwar, maimakon Naira Miliyan Dubu 250 da suka nema daga gwamnati biyo bayan rusau da gwamnatin kano ta yi musu tun farkon hawanta mulki.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta ce ta daukaka kara kan hukuncin da ta bayyana a matsayin rashin adalci.

Kwamishinan Shari’a na Jihar Barista Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotu ba ta yi daidai ba wajen yanke hukuncin ga kungiyar ‘yan kasuwa saboda dokar amfani da filaye a kowace jiha.

A karshe ya ce kotun ba ta da hurumin ko da sauraren ƙarar saboda gwamnati ce kadai ta mallaki fili kamar yadda dokar amfani da filaye ta tanada.

Post masu alaƙa

Hisbah za ta fara farautar masu aikata baɗala a Kano

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.